Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.
Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”
Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, ‘A gaishe ka!’ Wanda yake gyara gumaka ya yi sumul Yana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su. Wani yakan ce, ‘Haɗin ya yi kyau,’ Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.