Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 41:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri, Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru, Har da za mu ce kun yi daidai? Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan, Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 41:26
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi, Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faru Tun daga farko, har zuwa ƙarshe?


Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba, Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru, Ku faɗa mana yadda zai zama duka, Domin lokacin da ya faru mu mu sani.


Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a, Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna. Wane ne ya faɗi abin da zai faru, Ya kuma yi annabci tuntuni? Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa? Ba wani Allah sai ni.


Kirawo sauran al'umma, su zo ga shari'a. A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba? A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu? Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsu Don su tabbatar daidai suke, Su shaida gaskiyar maganganunsu.


Wane ne ya sa wannan ya faru? Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi? Ni Ubangiji, ina can tun da farko, Ni kuma Ubangiji Allah, Zan kasance a can har ƙarshe.


Ku tuna da abin da ya faru tuntuni, Ku sani, ni kaɗai ne Allah, Ba kuwa wani mai kama da ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ