Ishaya 41:25 - Littafi Mai Tsarki25 “Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas, Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa. Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka, Kamar yadda magini yake tattake yumɓu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.