Ishaya 41:2 - Littafi Mai Tsarki2 “Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas, Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi? Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai? Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura! Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 “Wa ya zuga wannan daga gabas, yana kiransa cikin adalci ga yin hidima? Ya miƙa masa al’ummai ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa. Ya mai da su ƙura da takobinsa, zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.