Ishaya 41:16 - Littafi Mai Tsarki16 Za ku watsa su sama cikin iska, Iska za ta hure su, ta tafi da su, Hadiri kuma zai warwatsar da su. Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku, Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.