Ishaya 41:15 - Littafi Mai Tsarki15 Zan sa ku zama kamar abin sussuka, Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini. Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su, Za a marmashe tuddai kamar ƙura. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.