suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.
Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.