Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 40:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 40:28
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka, Saninsa ya fi gaban aunawa.


Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni? Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba?


“Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.


Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”?


Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.


balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.


Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!


Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.


Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


Kafin a kafa tuddai, Kafin kuma ka sa duniya ta kasance, Kai Allah ne, Madawwami. Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.


“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.


Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana, Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.


Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce, “ ‘Na sa ka haske ga al'ummai, Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”


Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.”


Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini, Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada. Ka cikasa aikin da ka fara.


Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.


Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka, Madawwaman damatsansa suna tallafarka, Yana kore maka maƙiyanka, Ya ce, ‘Ka hallaka su!’


Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.”


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”


Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya.


Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


Kada ku zaci zan kawo jama'ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.


Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa, Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.


“Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.


Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”


Ko ka san iyakar fāɗin duniya? Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.


“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ