Ishaya 40:26 - Littafi Mai Tsarki26 Ka dubi sararin sama a bisa! Wane ne ya halicci taurarin da kake gani? Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji, Ya sani ko su guda nawa ne, Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202026 Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |