shi da yake yi mana ta'aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta'azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta'aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah.
“Zan ji juyayi a kan Sihiyona, Da dukan masu zama a kufanta. Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu, Kamar lambun da na dasa a Aidan. Murna da farin ciki za su kasance a can, Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.
Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.
Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
Sa'an nan ya ce musu, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha ruwan inabi mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi, gama wannan rana tsattsarka ce ta Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin da Ubangiji ya ba ku shi ne ƙarfinku.”
Ya aike ni in yi shela, Cewa lokaci ya yi Da Ubangiji zai ceci mutanensa, Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki,
Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta'azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”