Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 39:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 39:3
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,


“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina kawo muku Wata al'umma daga nesa,” in ji Ubangiji, “Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun zamanin dā. Al'umma wadda ba ku san harshenta ba, Ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.


A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.


Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.


cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.


A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”


Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da Amaziya. Ubangiji ya aiki annabi a wurinsa. Annabin ya ce masa, “Don me ka koma ga gumakan da ba su iya ceton jama'arsu daga hannunka ba?”


Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,


Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”


Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.


Ishaya ya ce, “Me suka gani a fāda?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Suka ga kome da kome. Ba abin da ban nuna musu ba a ɗakunan ajiya.”


“A faɗakar da al'ummai, yana zuwa, A faɗa wa Urushalima cewa, ‘Masu kawo mata yaƙi suna zuwa daga ƙasa mai nisa, Suna yi wa biranen Yahuza ihu.


Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ