Ishaya 39:2 - Littafi Mai Tsarki2 Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko'ina a mulkinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.