Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 38:5 - Littafi Mai Tsarki

5 cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 38:5
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Ka san irin wahalar da nake sha, Kana riƙe da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?


Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.


Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya, Yakan ɗaure raunukansu.


Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa, Abu mai daraja ne!


Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,


Sa'an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ji addu'arka, ya kuma amsa.”


‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”


Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abi, 'yar Zakariya.


Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’


ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’


“Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka kuma kasa kunne ga roƙona, Kada ka yi shiru sa'ad da na yi kuka gare ka! Yadda dukan kakannina suka yi, Ni baƙonka ne na ɗan lokaci.


Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can, An ƙayyade yawan watannin da zai yi, Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.


A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.


Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,


A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.


Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako, Yana kuwa amsa addu'o'ina.


Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.


Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.


Ka kuwa ji muryata. Kada ka rufe kunnenka ga jin kukana na neman taimako.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ