Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.
A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”