Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 38:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai. Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 38:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In kuwa Ubangiji ne yake hukunta mu, to, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.


Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”


Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni, Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!


Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin da yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā.


Ka aiko mini da wahala da azaba, Amma za ka mayar mini da ƙarfina, Za ka tashe ni daga kabari.


Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?


Ka ƙyale ni ko zan sami kwanciyar rai, Kafin in tafi, ai, tawa ta ƙāre.”


Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.


Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji, Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.


Ka dawo da ni daga lahira. Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa, Amma ka ceci raina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ