Ishaya 37:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ubangiji zai sa Sarkin Assuriya ya ji jita-jitar da za ta sa ya koma ƙasarsa, Ubangiji kuwa zai kashe shi a can.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.