Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 37:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 37:3
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Naƙudar haihuwarsa ta zo, Amma shi wawan yaro ne, Bai fito daga mahaifar ba.


Kada ku zaci zan kawo jama'ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, 'ya'ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.


Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala.


“Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba, Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra'ila, suka neme shi, suka same shi.


Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.


Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.


“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”


Kaito, gama wannan babbar rana ce, Ba kuma kamarta, Lokaci ne na wahala ga Yakubu, Duk da haka za a cece shi daga cikinta.”


Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama'arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!


Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji, A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.


“Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.


Ifraimu za ta zama kango a ranar hukunci. A kabilan Isra'ila na sanar da abin da zai faru, ba makawa.


sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ