Ishaya 37:24 - Littafi Mai Tsarki24 Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |