Ishaya 35:9 - Littafi Mai Tsarki9 Ba za a sami zakoki a can ba, Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba. Waɗancan da Ubangiji ya fansar Su za su zo gida ta wannan hanya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.