Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba.
Sa'ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana.
Ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama Saul, mahaifina ba zai same ka ba. Za ka zama Sarkin Isra'ila, ni kuma zan zama wazirinka. Saul mahaifina ya san da haka.”
“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.