Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 34:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 34:9
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.


Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.


Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.


amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka.


Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa, Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.


ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ