“Zan mayar muku da abin da kuka yi hasararsa A shekarun da fara ta cinye amfaninku, Wato ɗango da fara mai gaigayewa, da mai cinyewa, Su ne babbar rundunata wadda na aiko muku.
Sa'ad da Yehoshafat da jama'arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta.
Sai Asa da jama'ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske.