“Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa, “ ‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama, Zai yi magana daga wurin zamansa mai tsarki, Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfi ƙwarai, Zai yi ihu kamar masu matse 'ya'yan inabi, Zai yi gāba da dukan mazaunan duniya.
Za a ji hayaniya har iyakar duniya, Gama Ubangiji yana da ƙara game da al'ummai, Zai shiga hukunta wa dukan 'yan adam, Zai kashe mugaye da takobi, Ubangiji ya faɗa.’ ”
Kamar yadda iska take korar hayaƙi, Haka nan zai kore su, Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta, Haka nan mugaye za su hallaka a gaban Allah.