Ishaya 32:6 - Littafi Mai Tsarki6 Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.