Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 31:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye 'ya'yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 31:5
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai rufe ka da fikafikansa, Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu. Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.


Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta, Tana rufe da 'yan tsakinta, Ta buɗe fikafikanta, ta kama su, Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.


Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”


Zan kāre wannan birni in kiyaye shi, saboda girmana, domin kuma alkawarin da na yi wa bawana Dawuda.’ ”


Yakan taimake su, yă kuɓutar da su, Yakan cece su daga mugaye, Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.


Al'umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”


Allah yana zaune cikin birnin, Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau. Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.


‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa take ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni.


Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba’ ” Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.


duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.


Gama zan tsare wannan birni, in cece shi don kaina, da kuma don bawana Dawuda.”


Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.


Rana tana zuwa da jama'a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza. Birni ƙaƙƙarfa ne, Allah kansa yake tsare garukansa!


ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.


Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su, Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya, Ubangiji Allah zai busa ƙaho, Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.


An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza, Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.


Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”


Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya, Don masu kai da kawowa. Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi, Gama yanzu ni kaina na gani.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ