Ishaya 31:2 - Littafi Mai Tsarki2 Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala'i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.