Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can?
Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba'al. Suna kama da tankwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi Saboda maganganunsu na fariya. Za su zama abin ba'a a ƙasar Masar.”
A Tafanes rana za ta yi duhu, Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar, Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare, Za a rufe ta da gizagizai. 'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.
Amma Sarkin Assuriya ya gane Hosheya ya tayar masa, gama ya aiki manzanni wurin So, wato Sarkin Masar, ya kuma ƙi ya kai wa Sarkin Assuriya haraji kamar yadda ya saba yi kowace shekara, Saboda haka sai Sarkin Assuriya ya kama shi ya sa shi a kurkuku.
Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)
Irmiya ya ce, “Na karɓi saƙo daga wurin Ubangiji. An aiki jakada a cikin al'ummai cewa, ‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gāba da ita, Ku tasar mata da yaƙi!’
Annabcin Obadiya ke nan. Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom. Ubangiji ya aiki manzonsa wurin sauran al'umma, Mun kuwa ji saƙonsa cewa, “Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da Edom!”