Ishaya 30:29 - Littafi Mai Tsarki29 Amma ku, jama'ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”