Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 30:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 30:10
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.


Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al'umma.”


Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwan inabi, Kuka kuma umarci annabawa kada su isar da saƙona.


Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.”


Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,


Suna ta faɗa wa waɗanda suke raina maganar Ubangiji cewa, ‘Za ku zauna lafiya!’ Ga kowane mai bin nufin tattaurar zuciyarsa, ‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”


“Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, ‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,’ To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!


“Kada su yi wa'azi,” amma sun yi wa'azi. “Idan ba su yi wa'azi a kan abubuwan nan ba, Raini ba zai ƙare ba.


Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”


Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?” Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji.


Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya?


ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”


Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu kashedi, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan suna.”


Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.


Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne.


Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”


To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba?


Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama'a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”


Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.


Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.


(A dā a Isra'ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)


Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.


Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.


Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’


Zai ta yi maka godo? Zai yi maka magana da tattausar murya?


Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ