Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.
Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu. Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.
Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.