Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa.
A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.
Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, 'ya'yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su.
Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa'ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa'ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.
Na yawaita gwauraye, wato mata da mazansu suka mutu, Fiye da yashin teku. Na kawo wa uwayen samari mai hallakarwa da tsakar rana. Na sa azaba da razana su auka musu farat ɗaya.
Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu.