Na kuwa tambaye ta, ‘'Yar gidan wane ne ke?’ Ta ce, ‘Ni 'yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu.
Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,
Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.