Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da 'yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.
Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?” Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.
Sa'ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan 'yar'uwarsa, sa'ad da kuma ya ji maganar Rifkatu 'yar'uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.
Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,
Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”
Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.
Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,