Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.
Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.
Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”
Ubangiji ya ce, “Zan kawo masifa a duniya. Zan hukunta dukan mugaye saboda zunubansu. Zan ƙasƙantar da kowane mai girmankai. Zan hukunta kowane mai izgili da mai mugunta.
saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”
Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
Idan na hurta, cewa hakika mugu zai mutu, amma ba ka faɗakar da shi don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa ba, wannan mugun zai mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.
Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”