Ishaya 29:8 - Littafi Mai Tsarki8 Dukan al'ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci, amma sai ya farka, yunwan tana nan; kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa, amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa. Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.