Sai Musa ya kirayi Bezalel, da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima wanda Ubangiji ya ba shi hikima a zuciya, da duk wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo, ya yi aikin.
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!
Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha'ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi.