Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 28:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa'ad da masifa ta auko za a hallaka ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 28:18
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba.


Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.


Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.


Za a tattake girmankan bugaggun shugabannin nan.


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


Sai mala'ikan nan ya ce mini, “Ruwan nan da ka gani, a inda karuwar nan take a zaune, jama'a ce iri iri, da taro masu yawa, da al'ummai, da harsuna.


Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya.


Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”


Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?


Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.


‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.


Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.” Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar.


da kowace doguwar hasumiya, da ganuwar kowace kagara.


“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.


A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.


Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.”


Idanunmu sun gaji Da zuba ido a banza don samun taimako, Mun zuba ido Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.


ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska.


Zai shafe maƙiyansa da ambaliyar ruwa, Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwa cikin duhu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ