Ishaya 27:11 - Littafi Mai Tsarki11 Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su mata kuma su zo su yi itacen wuta da su. Gama mutane ne marar azanci; saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba, Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.