Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 26:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji, A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu; sa’ad da ka hore su, da ƙyar suna iya yin addu’a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 26:16
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.


Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.


Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare, Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarki Kamar ruwa gaban Ubangiji. Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi, Saboda rayukan 'ya'yanki, Waɗanda suke suma da yunwa A magamin kowane titi!


Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda suke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!


Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu.


Na kawo masa dukan koke-kokena, Na faɗa masa dukan wahalaina.


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.


Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.


Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.


Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’


Amma Isra'ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.”


Ka ce, “Zo wurina,” Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,


Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya. Sa'ad da nake tunani, Nakan ji kamar in fid da zuciya.


Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu, Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba, Suka yi addu'a sosai a gare shi.


Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ