Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 26:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba, Kurwarsu ba za ta tashi ba, Domin ka hukunta su, ka hallaka su. Ba wanda zai ƙara tunawa da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 26:14
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.


Mutane za su riƙa ce muku ku nemi shawarar 'yan bori da masu sihiri waɗanda suke shaƙe muryar, har ba a jin abin da suke faɗa. Za su ce, “Ai, ma, ya kamata mutane su nemi shawara daga aljannu, su kuma nemi shawarar matattu saboda masu rai.”


Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor, Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.


Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.


“Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.”


Me za ku yi sa'ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa'ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?


Ka sa dukan zuriyarsa su mutu, Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.


An hallaka abokan gābanmu har abada, Ka lalatar da biranensu, An kuma manta da su sarai.


Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana.


A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra'ilawa daga hannun Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar.


Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.


Dubi inda mugaye suka fāɗi! Can suka kwanta, ba su iya tashi.


Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni, Ka tashi ka hukunta al'ummai, Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!


Suna da kunnuwa, amma ba sa ji, Ba kuma numfashi a bakinsu.


Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam.


Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.


suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.


Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi, Haka nan mutum yake mutuwa.


Sunansa ya ƙare a gida da a jeji, Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.


Ba wanda zai tuna da shi, mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba. Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai. Za a sare mugunta kamar itace.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ