Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana cikin sauran al'umma inda mutanen Isra'ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra'ila, a gaban sauran al'umma kuma, sa'ad da na fito da mutanen Isra'ila, daga ƙasar Masar.
Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu. Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi! I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!
Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”