Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.
Ba wanda yake farin ciki a cikin sauruka masu dausayi. Ba wanda yake sowa ko waƙa a cikin gonakin inabi. Ba mai matse ruwan inabi, sowar murna ta ƙare.
Kana cikin Aidan, gonar Allah. An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja, Tare da zinariya. Kana da molo da abin busa. A ranar da aka halicce ka Suna nan cikakku.