Ishaya 24:7 - Littafi Mai Tsarki7 Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane; dukan masu farin ciki suna nishi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gonakin da suke kusa da Heshbon, da gonakin inabin da suke Sibma an lalatar da su, gonakin inabin nan waɗanda ruwan inabinsu suke sa masu mulkin al'ummai su bugu. Da kurangunsu sun taɓa yaɗuwa zuwa gabas har suka kai birnin Yazar da cikin hamada, wajen yamma kuma sai da suka dangana da gefen Tekun Gishiri.