Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.
Domin haka, ku duwatsun Isra'ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba'a ga al'umman da suke kewaye,
Sa'ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba'in, ta kiyaye asabatai.
Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.
Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”
Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.
A wannan rana za su yi karin magana a kanku, Za su yi kuka da baƙin ciki mai zafi, Su ce, “An lalatar da mu sarai! Ya sāke rabon mutanena, Ya kawar da shi daga gare ni! Ya ba da gonakinmu ga waɗanda suka ci mu da yaƙi.”