“Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Balle fa sa'ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba!
Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima.
Ka gayyato mini tsoro Kamar yadda akan gayyato taro a ranar idi. A ranar fushin Ubangiji Ba wanda ya tsere, ko wanda ya tsira. 'Ya'yan da na yi renonsu, na goye su, Maƙiyina ya hallaka su.