Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.
Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi. Dukan ƙofofinta sun zama kufai, Firistocinta suna nishi, Budurwanta kuma suna wahala, Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.
Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!
Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.
Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.