Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljannu, Matattarar kowane baƙin aljani, Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.
Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”
Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.
Sa'ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da take a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba.
Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.
Wannan shi ne jawabi a kan Taya. Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.
Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.
Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.