Dukan waɗanda suka san ka a cikin al'ummai Za su gigice saboda masifar da ta auko maka, Za ka zama barazana ga al'ummai, Ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su.
Domin lokacin hallaka dukan Filistiyawa ya yi. Za a datse wa Taya da Sidon kowane taimakon da ya ragu, Gama Ubangiji zai hallaka Filistiyawa Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.
“A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”