“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.
Allah ya ce, “Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe! Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a. Za ku sami zarafi ku yi magana. Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.