Mutanen Yahuza su uku suka fito don su tarye shi, shugaba mai lura da fāda, wato Eliyakim ɗan Hilkiya, da marubucin ɗakin shari'a, wato Shebna, da shugaban da yake kula da tarihin da aka rubuta, wato Yowa ɗan Asaf.
Ya aiki Eliyakim mai kula da fāda, da Shebna marubucin ɗakin shari'a, da manyan firistoci zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Su kuma suna saye da tsummoki.
Sa'an nan Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka kyakkece tufafinsu don baƙin ciki, suka tafi, suka faɗa wa sarki abin da shugaban mayaƙan Assuriya ya yi ta farfaɗa.
Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.
Sa'an nan sai Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka ce wa shugaba na Assuriya, “Ka yi mana magana da harshen Aramiyanci, muna jinsa. Kada ka yi da Ibrananci, dukan jama'ar da suke a kan garu suna saurare.”